Rubutun malamin addini ya ta da ƙura a shafin sada zumunta na Facebook
Daga Usama Taheer Maheer
A safiyar yau babban malamin addinin Musluncin, Prof. Masur Sakkwato, ya wallafa wani rubutu a shafinsa na kafar Facebook, inda yake bayyana jin daɗinsa a kan yadda wani mai suna ‘Victor’ ya dawo masa da wayar shi ƙirar ‘iPhone 12 pro’, wacce ta faɗi ba tare da saninsa ba, jiya a unguwar Zone 2 da ke Abuja.
Ba iya yaba wa matashin ya yi ba, ya yi ƙarin haske a kan cewa da Bahaushe Musulmi ne, ba lallai ya dawo da wannan wayar ba.
Ga rubutun da babban malamin ya sa a shafin nasa:
“Wayata ta faadi jiya, Victor ya tsinci wayata iPhone 12 pro da ta fadi a Zone 2, Abuja.
Victor bai yi wata wata ba da na kira shi ya kwatanta min inda yake na zo na karba.
Wai kuwa da hannun wani “Mamman” ta fada kuna ganin zan same ta?”
Tun bayan wannan rubutun, mutane da dama suka fara bayyana ra’ayinsu a kan rubutun.
Da yawan masu sharhi sun nuna rashin dacewar rubutun. A cewarsu, bai kamata babban malami kamar prof. Mansur Sakkwato ba wanda ke koyar da addini da tarbiyya ya fito kafar sada zumunta ya na irin wannan shaguɓen ba.
Hakan a fakaice yana nuna gazawarsu ne ta malamai a kan faɗakar da mutane, a cewar wasu masu amfani da kafar Facebook.
Yayin da wasu masu sharhin kuwa suke ganin abin da malamin ya rubuta daidai ne, domin in da bahaushe ne ya tsinci wayar ba zai taɓa dawowa da ita ba.
Yayin da wasu kuma ke ganin ita nagarta ba ruwanta da ƙabila ko addini. Ko Musulmi ko Kirista, ko Bahaushe ko Inyamuri duk wanda ya tsinci waya in dai nagari ne, zai iya dawowa da mai ita kayansa.
Ga wasu daga cikin martanin jama’a game da rubutun:
Sada Sulaiman yake cewa, “Malam ba shi da labarin Mamman ɗin da ya tsinci miliyoyin kuɗi ya mayar ne?”
Aliyu M Ahmad ya rubuta, “Hali, ba ruwansa da addini, sai dai addini yana koyar da kyakkyawan hali. Duk lalacewar zamani, akwai mutanen kirkir a kowanne rukunin al’umma, mun kuma tsammata kirki daga Musulmai”
Sai Datti Assalafi shima ya rubuta, “Ala Gafatta mallam kafadi gaskiya domin dayawan musulmai dai suna kawai suka tara.”
Jim kaɗan bayan waɗannan martani da ma wasu wanda suka haura dubu biyar, malamin ya sake sakin wani saƙo a shafin nasa inda ya ke bayyana cewa ra’ayi riga ce—kowa da irin tasa.
Kuma ya ƙara da cewa babu wanda zai iya hana faɗar ra’ayinsa, gaskiya ce dai da ba a som ya faɗa kuma dole sai ya faɗa.