Ronaldo ya kafa tarihi, ya zama ɗanwasan da ya fara zura ƙwallo 900 a raga
Daga Sabiu Abdullahi
Cristiano Ronaldo ya zama ɗan wasa na farko a tarihin kwallon ƙafa da ya zura kwallo 900 a ragar.
Wannan ya biyo bayan wasan Nations Lig da Portugal ta yi nasara kan Croatia a daren Alhamis.
Kwallon da Ronaldon ya ci a minti na 34, ya taimaka wa Portugal wajen sa kwallo biyu a raga.
Wannan ya sa ya zama ya ci kwallo 131 cikin wasanni 209, abin da ya sanya shi kafa tarihin fin kowa cin kwallo da buga wasanni a ƙasarsa.
Kididdiga ta nuna Messi ne na biyu a jerin da Ronaldo ke jan ragama sai kuma tsohon ɗan wasan Iran Ali Daei da ke da kwallo 109.