January 14, 2025

Rikicin Isra’ila da Hamas ya kai ga sakin mutanen da aka yi garkuwa da su, an kuma yi musanyar fursunoni

9
images-2023-11-24T213747.849.jpeg

Daga Sabiu Abdullahi

A lokaci guda, Isra’ila ta saki fursunonin Falasdinawa 39 a wani bangare na yarjejeniyar.

Wadanda aka yi garkuwa da su sun hada da ‘yan Isra’ila 13, ‘yan kasar Thailand 10, da kuma dan kasar Filifin guda daya.

Kwamitin kasa da kasa na kungiyar agaji ta Red Cross (ICRC) ya taimaka wajen jigilar wadanda aka kama daga Gaza zuwa kan iyakar Rafah da Masar.

Hukumar ta ICRC ta bayyana jin dadi kan yadda aka saki wadanda aka yi garkuwa da su a shafukan sada zumunta.

Wannan sakin wani bangare ne na wata yarjejeniya mai fadi tsakanin Isra’ila da Hamas, wanda ya hada da tsagaita wuta na kwanaki hudu da musayar wadanda aka kama.

Mutanen 24 da aka sake suna wakiltar wani kaso na kusan 240 da Hamas ta yi garkuwa da su a lokacin wani hari da aka kai a kudancin Isra’ila a ranar 7 ga Oktoba.

Firaiminista Benjamin Netanyahu, a cikin wani faifan bidiyo, ya tabbatar da kudurin gwamnati na tabbatar da dawowar duk wadanda suka yi garkuwa da su.

Qatar, wata babbar mai shiga tsakani, ta bayyana cewa, a wani bangare na yarjejeniyar, an saki mata da yara Falasdinawa 39 da ake tsare da su a gidajen yari na Isra’ila.

Isra’ila ta tabbatar da sakin fursunonin 39.

9 thoughts on “Rikicin Isra’ila da Hamas ya kai ga sakin mutanen da aka yi garkuwa da su, an kuma yi musanyar fursunoni

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *