Rikicin Gabas ta Tsakiya: Amurka na nan daram a bayan Isra’ila—Biden
Daga Sabiu Abdullahi
Shugaban Amurka Joe Biden ya bayyana cewa sojojin Amurka sun yi aiki tare da Isra’ila wajen kakkaɓo makaman Iran, yana mai cewa harin ba ya da wani tasiri saboda an dakile shi.
Biden ya kuma jaddada cikakken goyon bayan Amurka ga Isra’ila bayan Iran ta kai hari da makamai masu linzami.
Wata sanarwa daga ofishin Firaministan Burtaniya ta ce Sir Keir Starmer ya tattauna da shugaban gwamnatin Jamus, Olaf Scholz, da wasu shugabanni na ƙasashe biyu – manyan abokan Isra’ila – inda suka yi Allah-wadai da harin na Iran.
Hakazalika, Faransa da Japan sun nuna rashin jin daɗinsu game da wannan hari, amma sun buƙaci dukkan ɓangarorin su dakatar da tashin hankali.