February 12, 2025

Rikici na neman ɓarkewa tsakanin Kwankwaso da Abba—Gwamna ya daina amsa kiran maigidan nasa

7
16_30_16_images.jpg

Rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar NNPP mai mulki a Kano na neman tsananta, inda gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf, ya fara ƙin ɗaukar wayar jagoransa Rabi’u Musa Kwankwaso sannan ya ƙi halartar tarukan da Kwankwaso ya shirya.

Wannan alama ta “Abba tsaya da kafarka” na cigaba da samun tasiri ga gwamnan, yayin da ake ganin wasu na ƙoƙarin ganin ya ɗauki ikon jam’iyyar da ƙungiyar Kwankwasiyya daga hannun Kwankwaso.

Wasu majiyoyi ambato cewa tuni Abba ya fara amsa waɗannan kira, bayan da aka sanar da shi cewa kusan kashi 90 na nade-naden da yayi sun fito ne daga ɓangaren Kwankwaso.

Majiyoyi sun bayyana cewa Abba ba ya jin daɗin “ƙarfa-ƙarfa” da Kwankwaso yake masa, inda ya fara bijirewa waɗanda ke kira gare shi da ya tsaya da kafarsa domin cigaban siyasar sa da na jihar Kano baki ɗaya.

7 thoughts on “Rikici na neman ɓarkewa tsakanin Kwankwaso da Abba—Gwamna ya daina amsa kiran maigidan nasa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *