February 10, 2025

‘Riƙaƙƙen Ɗanta’adda Kachallah Bugaje Ya Tuba Daga Fashi Da Makami’

0
image_editor_output_image1744328321-17378363813881950209329095782535.jpg

Wani sanannen ɗan fashi da makami da aka sani da Kachallah Bugaje ya bayyana tubarsa daga aikata laifuka, ciki har da satar mutane da fashi, tare da mayaƙansa 50.

A cikin wani bidiyo mai tsawon minti 5 da daƙiƙa 42, ya sanar da sauya sunansa zuwa Zakiru Bugaje tare da alkawarin daina aikata miyagun laifuka.

Ya ce, “Ba a sake kirana da Kachallah Bugaje, yanzu sunana Zakiru Bugaje.” Ya kuma jaddada cewa ya yi watsi da dukan nau’in aikata laifi, yana mai cewa, “Ba zan sake yin sata ko garkuwa da mutane ba.”

Bugaje ya amsa cewa ya taɓa yin garkuwa da fiye da mutum 50 tare da neman kudin fansa daga iyalansu, inda wasu aka buƙaci su biya har naira miliyan 10 ko 25.

Sai dai ya bayyana cewa daga baya sun saki waɗanda suka yi garkuwa da su ba tare da karɓar ko kwabo ba.

Ya ce sun yi garkuwa da fiye da mutum 50, sun kuma kira iyalansu, wasu mun ce su biya miliyan 10, wasu miliyan 25, amma daga baya sun kira iyalansu sun sake su ba tare da karɓar ko kwabo ba.

A cewarsa, sun yanke shawarar sakin su ne saboda tsoron Allah da kuma alfarmar Annabi Muhammad (SAW).

A tsawon bidiyon, Bugaje ya ci gaba da yin Allah-wadai da laifukan da ya aikata a baya tare da jinjina ga Annabi Muhammadu (SAW).

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *