Real Madrid ta tabbatar da ci gaba da zaman Modric da Vazquez a Santiago
Daga Sabiu Abdullahi
Daga Sabiu Abdullahi
Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta shirya tsawaita kwantiragin wasu manyan ‘yan wasanta guda biyu wato Luka Modric da Lucas Vazquez.
A cewar majiyoyin, an kammala harkallar, kuma ana gab da fitar da sanarwa daga kungiyar a hukumance.
“Luka Modric da Lucas Vazquez dukkansu suna nan daram,” wata majiya ta tabbatar da cewa duk kwantiragin an gama da su.
Wannan labari dai zai zo wa magoya bayan kungiyar ta Real Madrid da dadi, domin ‘yan wasan biyu sun taka rawar gani a nasarar da kungiyar ta samu a shekarun baya.
Modric, dan wasan tsakiya, ya kasance jigo a kungiyar tun shekara ta 2012, yayin da Vazquez, dan wasan gefen baya, ya kasance a kungiyar tun shekarar 2015.