Rayuwar IBB: Darusa da Ƙalubale Ga Ƴan Siyasa

Daga Salman Isah
Yawancin mutane sun fi riƙe labarin ƙage, sharri da kuma ɓatanci da suka ji akan wani mutum ba tare da tantance gaskiyar abinda aka faɗa musu akan sa ba, ko kuma bincika alaƙar dake tsakanin wancan da kuma wanda ya ba su labarin.
Wani ya taɓa gani na da Alhajin unguwar su muna taɗin kwallo bayan sallar Asuba, da muka isar sai yace min ‘Ya aka yi ka saba da wannan matsolon Alhajin? Ai baƙin marowaci ne, idan ka ga ka ci kuɗin sa to faɗuwa suka yi.’
Nace masa yaya aka yi ka san yana da rowa? Yace ai tunda suke unguwa ɗaya bai taɓa ma ba shi ko kwandala ba. Nace mishi dama Allah ya aiko shi ya ba ka ne ko kuma an ce ka nemi naka? Ko kuwa kwadago ka yi masa bai biya ka ba?
Duk da irin manyan ayyukan raya ƙasa da gina Najeriya ta hanyar ƙirƙiro sabbin jihohi, ma’aikatu da hukumomin gwamnati da cibiyoyin tsaro da gwamnatin sa ta yi a lokacin mulkin sa, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, IBB, bai samu shaida ta kwarai daga bakin yawancin mutane ba musamman a Arewacin Najeriya saboda dalilai biyu. Na farko labaran ƙanzon kurege da aka yi ta yi akan sa, sai waɗanda a baya makauniyar soyayyar Buhari ta sa suke jin haushin IBB saboda tumɓuke gwamnatin mulkin soja ƙarƙashin dogo ɗan Daura.
Shi kuwa IBB, bai taɓa fitowa fili don wayar da kan al’umma su so shi ba, balle yace musu labaran da kuke ji a kai na fa ƙage ne, bai kuma taɓa yi musu gorin ayyukan da gwamnatin sa ta yi ba. Har sai da lokaci yayi da gaskiya ta bayyana.
Baya ga haka, abinda yawancin mutane ba su sani ba sai yau shine irin tallafawa fitattun yan kasuwa da waɗanda ake kallo a matsayin masu dukiya da IBB yayi a lokacin mulkin sa (a lokacin da su kuma suke tasowa/gwagwarmaya), amma ko da wasa bai taɓa cewa Na taimaki Ɗangote, Arthur Eze , dss ba.
Darussa:
1. Kada ka ɗauki zancen mutane akan wani mutum, yi amfani da abinda ya bayyana maka.
2. Kada ka damu sai ka nunawa mutane cewa kai mutumin kirki ne, cigaba da aikata kirkin ko za’a kushe.
3. Taimaki al’ummar ka ta hanyar tallafa musu a harkokin kasuwanci da sana’o’in su.
4. Ƙauracewa yawan koke musamman idan kana jagoranci.
5. Ka zama jajirtacce kan abinda ka tabbatar kuma ka yi imanin shine gaskiya, har sai lokacin da akasin haka ya bayyana maka.
6. Ka guji gori yana jawo ƙasƙanci.
Salmanu Isah Darazo
Febrairu 20, 2025.