January 13, 2025

#RashinTsaroAArewa:Ƴan daba sun kai farmaƙi wa jami’an NAFDAC a Abuja

0
New-Project-2024-02-12T165010.884.jpg

Daga Sabiu Abdullahi

A ranar Litinin ne wasu gungun ‘yan daba ne suka ƙaddamar da farmaki kan jami’an hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC) da ke gudanar da aikin tabbatar ingancin magani a Abuja.

Kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito, lamarin ya faru ne a yayin wani samame da aka kai a tashar mota ta Area 1.

‘Yan iskan sun muzanta jami’an tsaron da ke rakiyar tare da jami’an hukumar, inda suka yi ta jifan motarsu da duwatsu, lamarin da ya yi sanadin farfasa gilashin motar.

Lamarin dai ya ta’azzara har jami’an ‘yan sanda suka shiga tsakani, inda suka yi ta harbin iska tare da harba barkonon tsohuwa domin tarwatsa ’yan dabar.

Sai dai ana cikin hakan ‘yan jarida da jami’an na NAFDAC suka samu damar tserewa daga wajen.

Shugaban tawagar, Mista Umar-Ahmed Suleiman, mataimakin shugaban hukumar ta NAFDAC, ya ce sun kai farmakin ya biyo bayan bayanan sirri da hukumar ta samu na yawan magunguna marasa inganci a wannan wajen.

Sai dai har yanzu TCR Hausa ba ta samu wani bayani da ƴan sandan Abuja suka fitar game da lamarin ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *