July 12, 2025

Rashin tsaro: Hafsoshin tsaro sun isa zauren majalisa domin amsa gayyatar da aka yi musu

images-123.jpeg

Daga Sabiu Abdullahi

Shugabannin hukumomin tsaron a Najeriya sun isa zauren majalisar ƙasar a ranar Laraba domin mayar amsa gayyatar majalisar dattawan na yin tattaunawa game da yadda matsalar tsaro ke kara ta’azzara.

Sun isa zauren majalisar ne da misalin karfe 12:39 domin ganawa da kwamitin daukacin Sanatoci.

Gayyatar jami’an tsaron dai na zuwa ne a lokacin da rashin tsaro da ake fama da shi a kasar ke ƙara ta’azzara.

Shugabanni tsaron da ake gayyata sun hada da hafsoshin sojin sama da ƙasa da ruwan Najeriya.