Rashin lantarki ya sa gawarwaki na ta ruɓewa a ɗakunan ajiya gawa na barikin soja—Lagbaja
Daga Sabiu Abdullahi
Rashin wutar lantarki a barikin sojojin Najeriya ya haifar da ruɓewar gawarwakin da ke dakin ajiyar gawarwaki.
Babban hafsan sojin kasa Najeriya, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja, ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a yayin da yake neman sa hannun ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu.
Ya kuma yi kira da a biya bashin wutar lantarkin da ake bin sojojin Najeriyar na naira biliyan 42.
Wannan bukata ta zo ne bayan da kamfanonin samar da wutar lantarki suka yanke wutar barikin Sojoji da dama.