Rasha ta yi hasarar sojoji sama da 70,000 a yaƙinta da Ukraine
Daga Sabiu Abdullahi
Rundunar sojojin Rasha ta yi asarar sojoji sama da 70,000 a yakin da suka yi da Ukraine cikin watanni biyun da suka gabata.
Wasu alkaluma daga ma’aikatar tsaro ta Biritaniya ne suka bayyana haka, inda suka ambato wasu majiyoyin leken asiri.
A cikin watan Mayu adadin sojojin da aka kashe da jikkata ya kai 1,262, a cewar ma’aikata cikin wani sakon da ta wallafa a dandalin sada zumunta na X.
Sanarwar ta ce, Rasha ta bude wani sabon fanni a yankin Kharkiv tare da ci gaba da kai hare-hare iri daya a sauran bangarorin.
A halin da ake ciki kuma, Ukraine na kare kanta daga mamayar Rasha tun watan Fabrairun 2022.
Tun daga wannan lokacin, ma’aikatar tsaron Burtaniya ta ke buga bayanai a-kai-a-kai kan yadda yakin ke gudana.
Biritaniya tana nuna matukar goyon bayan tsaro ga Ukraine.
Sai dai ita Moscow ta zargi London da rashin gaskiya.
Inspiring qyest there. Whhat occurred after? Good luck!