Ranar Talata babu aiki a Najeriya saboda bikin samun ƴancin kai na 1 ga Oktoba

Daga Sodiqat A’isha Umar
Gwamnatin Tarayya ta ayyana Talata, 1 ga watan Oktoba a matsayin ranar hutu cikar Nijeriya shekara 64 da samun ’yancin kai.
Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da Babbar Sakatariyar Ma’aikatar, Dokta Magdalene Ajani, ta fitar a ranar Asabar din nan.
Ministan ya ce duk tarin kalubalen da kasar nan ke fuskanta, gwamnati na iya bakin kokarinta wajen ganin ta magance su.
Ministan ya kuma taya dukkan ’yan kasar na gida da na ketare murnar zagayowar ranar da kasar nan ta samun yacin kanta daga turwar mulki mallaka.
Hi tthere it’s me, I am also visiting this website regularly, this site is eally pleasant annd the visitors aare inn fasct sharring goodd
thoughts.