December 7, 2025

Raina ya ɓaci ganin irin abincin da ake rabawa na Azumi a Jihar Kano—Abba Kabir

FB_IMG_1711209394195.jpg

Daga Sabiu Abdullahi

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya nuna rashin gamsuwarta game da yadda ake gudanar da aikin shirin raba abincin azumin Ramadan da ake yi a jihar.

Ya nuna hakan ne a wata ziyarar ba-zata da ya kai ɗaya daga cibiyoyin da ake aikin raba abincin a Ƙaramar Hukumar Municipal, gwamnan ya nuna rashin jin dadi game da irin abincin da ya gani ana rabawa a cibiyar.

An jiyo shi uana cewa “manja suke samu ku ba miya ba?”

Gwamnan ya kuma nuna damuwarsa kan yawa da kuma ingancin abinci da ya ga ana ba wa mutane, wanda a cewarsa ya sha banban da abin da gwamnatinsa ta amince ta kuma sahale a dinga bayarwa.

“Wannan wane irin shirme ne,” in ji gwamnan lokacin da yake zantawa da masu dafa abincin.

Ya kuma tambaye su wane ne ya ba su damar dafa abincin a wannan tsari.

5 thoughts on “Raina ya ɓaci ganin irin abincin da ake rabawa na Azumi a Jihar Kano—Abba Kabir

Comments are closed.