December 7, 2025

Rafofin Firimiya za su fara bayani dalla-dalla wa magoya baya kan hukuncin VAR da zarar an gama wasa

images-2024-01-30T184921.682.jpeg

Daga Sabiu Abdullahi

Daga kakar wasa mai zuwa, alkalan wasa a gasar Firimiya za su riƙa yin bayanin game da hukuncin na’urar VAR ta yanke ga magoya bayan da ke cikin filin wasa.

A cewar Mail Sport, IFAB ta amince da jami’an wasa su ba da bayani a wasanni bayan nasarar gwajin da aka yi a Mexico da Portugal.

Ana sa ran za a tabbatar da wannan ƙudiri a gaban AGM a watan Maris.

Shugaban alkalan gasar Premier, Howard Webb, ya kasance mai nuna cikakkiyar goyon baya wajen nuna gaskiya a wasanni tun lokacin da ya shiga PGMOL a 2022.