January 15, 2025

Peter Obi ya soki Tinubu kan sake sayen jirgin sama

0
images (8) (31)

Daga Sabiu Abdullahi  

Tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour a zaɓen 2023, Peter Obi, ya yi kira ga shugaban kasa Bola Tinubu da ya bayyana hakikanin kudin da aka kashe da kuma jimawar sabon jirgin da aka sayo, a dai dai lokacin da ake ta sukar gwamnatin kasar kan sayen jirgin a lokacin da ake cikin mawuyacin hali na tattalin arziki.  

Obi, tsohon gwamnan jihar Anambra, ya yi wannan kira ne a jerin saƙonnin da ya tura a kafar X, inda ya jaddada cewa gaskiya da rikon amana ya kamata su zama alamar kowane shugabanci na gaskiya.

Ya kuma bukaci a ba da bayanai kan yadda aka yi watsi da tsofaffin jiragen shugaban kasa da suka hada da adadinsu da shekarun da suka yi da kuma dalilin sayar da su.  

“Gwamnati ba za ta rasa komai ba sai mutuncinta, idan ta kasa samar da isassun bayanai game da shugabancinta ga mutanen da ake amfani da kudadensu, kuma waɗanda da bazarsu ake rawa,” inji Obi.  

Har yanzu dai ana ta tafka muhawara a kafafen sada zumunta game da sayen sabon jirgin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *