May 17, 2025

PDP Ta Lashe Zaɓen Kananan Hukumomi 30 a Jihar Osun

images-2025-02-22T204947.490.jpeg

Jam’iyyar PDP ta samu nasara a dukkan ƙananan hukumomi 30 na jihar Osun da ke kudu maso yammacin Najeriya, tare da lashe kujerun kansiloli gaba ɗaya.

Tashar Channels ta ruwaito cewa shugaban hukumar zaɓen jihar mai zaman kanta, Hashim Abioye, ne ya bayyana sakamakon yayin wata ganawa da manema labarai.

Tun kafin zaɓen, rikici ya ɓarke tsakanin gwamnatin jihar, rundunar ‘yan sanda, da ma ministan shari’a na ƙasa. Ministan ya nemi a dakatar da zaɓen, yayin da ‘yan sanda suka ce sun samu bayanan sirri kan yiwuwar tayar da tarzoma. Sai dai, gwamnan ya ƙi amincewa da wannan buƙata, yana mai cewa zaɓen zai ci gaba kamar yadda aka tsara.

2 thoughts on “PDP Ta Lashe Zaɓen Kananan Hukumomi 30 a Jihar Osun

Comments are closed.