January 14, 2025

PDP ta lashe zaɓen duka ƙananan hukumomi 20 na Jihar Bauchi

0
IMG-20240818-WA0022

Daga Abdullahi I. Adam

Sakamakon zaɓen ƙananan hukumomi da aka gudanar ranar Asabar ɗin nan a jihar Bauchi ya nuna cewa jam’iyyar PDP da ke mulkin jihar ce ta lashe dukkanin kujerun a ƙananan hukumomin jihar 20 da ke faɗin jihar.Zaɓen wanda aka gudanar a jiya Asabar 17 ga watan Agusta, ya ci karo da ƙarancin masu kaɗa ƙuri’a kamar yadda rahotanni suka nuna.A daren da ya gabata ne shugaban hukumar zaɓen jihar, Ahmed Makama ya bayyana sakamakon zaɓen a birnin Bauchi bayan tattara alƙaluma.Rahotanni sun nuna cewa jam’iyyar APC ta jihar ta yi watsi da wannan sakamako wanda ta bayyana a matsayin ‘fashi kan ‘yancin masu zaɓe da kuma cutar da tsarin dimokraɗiyya”.Sai dai kuma a nata ɓangaren jam’iyyar APC ta zargi jam’iyyar PDP da sauya sakamakon zaɓen a wani taron manema labarai da ta kira sakatariyarta da ke birnin na Bauchi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *