December 7, 2025

PDP Ta Kori Wike, Fayose, Anyanwu Da Wasu Jiga-jigan Jam’iyyar

Screenshot-501

Daga Sabiu Abdullahi

Jam’iyyar PDP ta kori Nyesom Wike, Ministan Babban Birnin Tarayya; Samuel Anyanwu, sakataren jam’iyyar da aka dakatar; da Ayo Fayose, tsohon gwamnan Ekiti.

An sanar da korar tasu ne a ranar Asabar yayin gangamin taron kolin jam’iyyar da aka gudanar a Ibadan, babban birnin Jihar Oyo.

Sauran da aka sallama daga jam’iyyar sun haɗa da Umar Bature, Ajibade Kamarudeen, Mao Ohabunwa, Uwachukwu, George Turner, Dan Orbih, Mohammed Abdulrahman, Austin Nwachukwu da Abraham Amah.

Tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar na kudu, Olabode George, shi ne ya gabatar da kudirin korar, sannan shugaban PDP na Bauchi, Samaila Buga, ya mara masa baya.

Gwamnan Bauchi kuma shugaban PDP Governors’ Forum, Bala Mohammed, shi ne ya jagoranci kada kuri’ar murya da aka yi domin tabbatar da hukuncin.