February 10, 2025

Paul Pogba zai dawo buga ƙwallo bayan ya sha hukuncin dakatarwa

310
FB_IMG_1728074612844

Daga Sabiu Abdullahi

An rage hukuncin dakatarwa da aka yanke wa ɗan wasan tsakiyar ƙasar Faransa, Paul Pogba, zuwa wata 18 bayan nasarar da ya samu a ƙarar da ya ɗaukaka a kotun wasanni.

Wasu majiyoyi na kusa da ɗan wasan Juventus sun shaida wa BBC Sport cewa zai iya dawowa yin atisaye a watan Janairu 2025, kuma zai samu damar komawa filin wasa a watan Maris.

Hukumar da ke yaƙi da shan ƙwayoyi masu ƙara kuzari ta Italiya ce ta dakatar da Pogba a watan Fabrairu bayan gwajin da aka yi ya nuna cewa ƙwayoyin halitta masu kuzari na namiji sun yi yawa a jininsa.

Shugaban kotun Cas, Matthieu Reeb, ya sanar da kamfanin labarai na Reuters cewa an rage dakatarwar zuwa wata 18 tun daga ranar 11 ga Satumba.

Tsohon ɗan wasan Manchester United ya shigar da ƙara da kansa a kotun Cas kuma ya gabatar da hujjoji a wani zama da aka yi a farkon wannan kakar.

Tun da farko ya sha faɗa cewa ba zai taɓa shan ƙwayar kuzari “da gangan ba,” kuma hukuncin da aka yanke masa “ba daidai ba ne.”

Da ba a rage masa dakatarwar ba, ba zai koma taka leda ba har sai a shekara ta 2027, lokacin yana da shekara 34 da haihuwa.

310 thoughts on “Paul Pogba zai dawo buga ƙwallo bayan ya sha hukuncin dakatarwa

  1. купить оригинальный диплом о высшем образовании [url=https://diplomdarom.ru/]купить оригинальный диплом о высшем образовании[/url] .

  2. дипломы о высшем образовании вуза купить срочно [url=https://4russkiy365-diplomy.ru/]дипломы о высшем образовании вуза купить срочно[/url] .

  3. продамус промокод скидка на подключение [url=https://promokod-pro.ru/]продамус промокод скидка на подключение[/url] .

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *