Pantami ya zargi jami’an tsaro da rashin amfani da tsarin NIN wajen kamo masu aikata laifuka
Daga Sabiu Abdullahi
Tsohon ministan sadarwa na Najeriya, Isa Ali Pantami, ya zargi rundunar ‘yan sandan Najeriya da sauran hukumomin tsaro da rashin amfani da tsarin NIN-SIM wajen yaki da rashin tsaro.
Pantami ya yi iƙirarin cewa manufar ta kasance babbar matsala, kuma ya kamata hukumomin da abin ya shafa da ke yaƙi da aikata laifuka su tabbatar da yin amfani da shi yadda ya kamata idan aka aikata laifi.
Ya ce rashin amfani da shi ne babbar matsalar.
Pantami ya roki Ubangiji Madaukakin Sarki da ya kubutar da duk wadanda aka yi garkuwa da su ya kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali a Najeriya.