January 14, 2025

Pantami ya roƙi matashin da ya hayo keke don ziyartarsa a Abuja daga Gombe da ya dakata a Bauchi

13
image_editor_output_image915352978-1716880225691.jpg

Daga Abdullahi I. Adam

Wani matashi mazaunin Gombe mai suna Auwal ya ƙudiri aniyar ziyartan babban shehin malamin nan, Shaikh Isah Ali Ibrahim Pantami, a Abuja a kan keke.

Kamar yadda wani na kusa da Shaikh Pantamin, Dr. Yakubu Sani Wudil ya wallafa a shafinsa na Facebook, a halin yanzu Auwal ɗin har ya isa Bauchi haye kan keke, kuma yana sa ran isa birnin na Abuja ba tare da wani ɓata lokaci ba.

Sai dai bayan shi Shaikh Pantami ya sami labarin, ya nuna rashin amincewarsa da ziyarar kuma ya roƙi matashin da ya janje wannan ƙudiri nasa, sannan ya dakata a Bauchi.

Shaikh Pantami ya rubuta, a shafinsa na Facebook cewa “Allah Ya ƙara mana ƙaunar juna. Allah Ya saka da alheri Dr Yakubu Sani Wudil da ka ankarar da ni kan wannan abu. Ina roƙon Malam Auwal ya tsaya daga Bauchin, a gidana dake gefen Masjidul Qur’an.”

Shehin ya tabbatar ma matsahin cewa za’a karɓe shi hannu bibiyu a Bauchin kuma za’a gana da shi a madadinsa sannan ya nemi Auwal da ya koma gida don kare lafiyarsa da mutuncinsa.

Har ila yau, Shaikh Pantamin ya umurci waɗanda za su tarbi Auwal ɗin cewa idan sun kammala tattaunawa da shi, su sa shi a mota tare da kekensa zuwa Gombe, kuma ya masa godiya sosai tare da fatan Allah Ya biya shi da gidan Aljannah.

Irin waɗannan ziyarori da matasa kan kai ma shahararrun mutane su kan sami rashin amincewa a baya-bayan nan, ba kamar a shekarun baya ba da matasan kan sami tarba ta mutunci da karraramawa ba kamar yadda su ka riƙa samu a baya.

13 thoughts on “Pantami ya roƙi matashin da ya hayo keke don ziyartarsa a Abuja daga Gombe da ya dakata a Bauchi

  1. and just… never leave until your return flight home (no shame!).エロ 下着The Big Apple has a wide selection of gorgeous accommodations — from trendy boutique properties downtown and in Brooklyn to historic hotels on the Upper East Side — so you won’t have any trouble finding an exceptional home base for your trip.

  2. 中国 えろこのレベルのカスタマイズは他では見られないもので、あなたの個々の好みに完全に合わせたドールを作成することができます.カスタマイズプロセスはユーザーフレンドリーで、分かりやすいガイドとサポートが用意されており、技術的なスキルがなくても理想のドールを作成することができます.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *