OPEC Ta Jinjinawa Tasirin Man Fetur na Matatar Dangote a Kasuwar Turai

Daga Sabiu Abdullahi
Ƙungiyar ƙasashe masu arzikin man fetur ta OPEC ta bayyana cewa man fetur da matatar Dangote ke samarwa yana da tasiri sosai a kasuwar man fetur, musamman a yankin Turai.
Matatar Dangote, wacce ke da ƙarfin samar da ganga dubu 500 a kowace rana, ta fara aiki a watan Janairun bara, sannan ta fara samar da man fetur a watan Satumba.
An bayyana cewa matatar na dogaro da ɗanyen mai daga ƙasashen wajen don samar da mai, abin da ke shafar harkokin kasuwancin man fetur a duniya kai tsaye.
Duk da wannan yabo, Injiniya Yabagi Sani, masani kan harkokin makamashi, ya ce kalaman na OPEC ba sabon abu ba ne kuma ba abin mamaki bane a gare su.