January 14, 2025

Opay ya sanar da sabon harajin tura kuɗin da ya kai ₦10,000

0
images (25)

Daga Sabiu Abdullahi  

Opay, babban kamfanin fintek a Najeriya, ya sanar da kwastomominsa wani sabon haraji kan musayar kuɗi.  

Daga ranar 9 ga Satumba, 2024, za a fara cajar kuɗi har N50 idan aka tura maka kuɗi N10,000 ko sama da haka. 

A cewar Opay, harajin zai bi ka’idojin Hukumar Harajin Harajin Cikin Gida ta Tarayya (FIRS) kuma za a miƙa kuɗin ne ga Gwamnatin Tarayya gaba ɗaya.  

Kamfanin ya sake nanata cewa ba zai amfana da cajin ta kowace hanya ba  

An shawarci abokan ciniki da su lura da sabon cajin kuma su sanya shi a ransu.  

Kaddamar da wannan harajin na zuwa ne a daidai lokacin da Gwamnatin Tarayya ke ci gaba da zakulo sabbin hanyoyin samun kudaden shiga domin bunkasa kudadenta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *