May 17, 2025

Ododo ya lashe zaɓen gwamnan Kogi

APCs-Ododo-wins-Kogi-guber-election-1024x576.jpg

Daga Sabiu Abdullahi

Usman Ododo, dan takarar gwamna na jam’iyyar APC, ya samu nasarar lashe kujerar gwamnan jihar Kogi bayan kammala zaben da aka gudanar a ranar 11 ga watan Nuwamba, 2023.

Ododo ya samu kuri’u 446,237, wanda ya zarce abokin hamayyarsa na kusa, Murtala Ajaka, na jam’iyyar Social Democratic Party (SDP), wanda ya samu kuri’u 259,052.

Dino Melaye, mai wakiltar jam’iyyar PDP, ya samu kuri’u 46,362, inda ya zo na baya-baya a zaɓen.

Wannan sanarwar ta zo ne a daidai lokacin da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta yanke shawarar gudanar da sabbin zaɓuka a wasu runfunan zabe a karamar hukumar Ogori/Magongo a ranar 18 ga watan Nuwamba, 2023.