NYSC: Gwamnati Ta Yi Wa Ƴan Bautar Ƙasa Alkawari

Masu yi wa ƙasa hidima (NYSC) za su kammala hidimarsu a Najeriya, yayin da gwamnatin ƙasa ta tabbatar da biyan cikon alawus mafi ƙaranci na watannin baya da ba a biya su ba.
Duk da cewa ba a bayyana takamaiman ranar da za a fara biyan kuɗin ba, ministan ci gaban matasa, Ayodele Olawande, ya tabbatar da cewa gwamnati za ta cika wannan alƙawari yayin wata hira da ya yi da gidan talabijin na Channels a ranar Talata.
Tun a watan Satumba 2024 ne gwamnati ta amince da sabon alawus mafi ƙaranci na Naira 77,000, daga Naira 33,000 da ake biya, amma har yanzu masu yi wa ƙasa hidima ba su fara karɓan sabon kuɗin ba.
Sai dai ana sa ran a watan Maris da muke ciki ne za a fara biyan su.
Wannan na faruwa ne a daidai lokacin da ‘yan Najeriya ke fama da tsadar rayuwa sakamakon hauhawar farashin kayayyaki, wanda ya biyo bayan janye tallafin man fetur da wasu manufofin gwamnati.
A yayin da wasu ke ganin ƙarin alawus ɗin zai rage wa matasa raɗaɗin tattalin arziki, wasu masu sharhi na ganin cewa ba zai wadatar ba, duba da yadda hauhawar farashin kayayyaki ke ci gaba da ƙaruwa.