NPC ta karyata labaran da ke nuna cewa tana ɗaukar sabbin ma’aikata
Hukumar Ƙidaya ta ƙasa (NPC) ta ƙaryata labarin da ke yawo a shafukan sada zumunta wanda ke nuni da cewa tana ɗibar sabbin ma’aikata.
A wasiƙar da ta wallafa a shafinta wanda ke ɗauke da sa hannun jami’inta mai kula da harkokin jama’a, Isiaya Yahaya, hukumar ta bayyana cewa, wasiƙar da wasu ke yaɗawa a kan cewa tana ɗiban sabbin ma’aikata ta bogi ce.
Ta ƙara da cewa, ta ɗebi ma’aikata tun a baya kafin a ɗage ƙidaya a karon farko.
Yanzu haka hukumar na jiran umarni daga shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tunubu, kan sabon lokacin da za a gudanar da ƙidayar.
A ƙarshe sun shawarci jama’a da su daina, yaɗa labaran ƙarya.
Bugu da ƙari duk labarin da ba su buga a.shafinsu ba, ba su san da shi ba.
Don haka a bibiyi shafukansu na sada zumunta domin samun sahihan labarai a kan cigaba game da ƙidayar, irinta ta farko da za a gudanar a zamanance, a faɗin Nigeria.