NNPP Ta Ce Kwankwaso Ne Zai Zama Shugaban Kasa A 2027

Jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) ta bayyana cewa za ta zama jam’iyya mai mulki a Najeriya nan da shekarar 2027.
Shugaban jam’iyyar na kasa, Dr. Ajuki Ahmad, ne ya bayyana hakan a taron kwamitin zartarwa na jam’iyyar (NEC) da aka gudanar a Abuja a ranar Alhamis.
A cewarsa, jagoran jam’iyyar, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, zai zama Shugaban Najeriya a 2027.
Duk da rikicin da jam’iyyar ke fuskanta, shugaban NNPP ya ce akwai zaman lafiya da kwanciyar hankali a mafi yawan rassan jam’iyyar.
“Jam’iyyarmu, ba shakka, tana fuskantar ƙalubale kaɗan, amma ba matsala ce mai wahalar magancewa ba. Ba kamar wasu jam’iyyu ba, da matsalolinsu ke barazana ga cigabansu, namu ba abu ne mai yawa ba. Wadanda suka yanke shawarar rabuwa da mu ba su da wata hujja ta doka, siyasa ko dabi’a da za su iya cutar da mu,” in ji shi.
“Saboda haka, ina kira ga shugabanninmu a dukkan matakai—na ƙasa, jihohi, ƙananan hukumomi da mazabu—da su jajirce wajen fuskantar waɗannan ƙalubale, musamman su yi watsi da ikirarin wasu da ke cewa sun kafa sabon shugabanci a Apapa, Lagos. Takardar da suke yadawa kamar wata babbar.”
“Mu tsaya tsayin daka a matsayin jam’iyya, mu ci gaba tare, mu yi aiki tare a matsayin tsintsiya maɗaurinki ɗaya, tare da buri guda.
gizli su kaçağı tespiti Su kaçağını tespit etmek için gelen ekip çok bilgiliydi. Tüm sorularımızı sabırla yanıtladılar. Tuncay Z. http://www.lostandfoundstudio.it/lfs/?p=10617
an73gc