NLC Ta Buƙaci Kamfanonin Sadarwa Su Janye Ƙarin Farashin Katin Waya Da Data

Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) ta bukaci kamfanonin sadarwa da ke aiki a kasar da su janye karin farashin da suka yi nan take tare da komawa tsohon farashi.
A wata sanarwa da ta fitar bayan taron da ta gudanar a ranar Talata a birnin Lokoja, jihar Kogi, NLC ta dauki matakai masu tsauri domin tunkarar lamarin. Kungiyar ta bukaci kamfanonin sadarwa su janye karin farashi tare da komawa tsohon farashi har sai kwamitin da ta kafa ya kammala bincikensa.
Haka kuma, NLC ta bukaci ma’aikatan Najeriya da sauran ‘yan kasa da su kaurace wa kiran waya ko amfani da data na kamfanonin MTN, Airtel, da Glo daga karfe 11:00 na safe zuwa 2:00 na rana kowace rana har zuwa karshen watan Fabrairu. Ta kuma umarci ‘yan Najeriya da su dakatar da sayen data daga wadannan kamfanoni.
Sanarwar ta kara da cewa dole ne kamfanonin sadarwa su mayar da kudaden da suka kwashe daga ‘yan Najeriya. Kungiyar ta yi gargadi cewa za ta jagoranci rufe ayyukan kamfanonin sadarwa a ranar 1 ga watan Maris idan har ba su janye karin farashin ba kafin karshen watan Fabrairu.
Bugu da kari, kungiyar ta umarci dukkan rassanta na jihohi da su zaburar da mambobinsu gabanin ranar 1 ga watan Maris tare da bukatar dukkan sauran sassan kungiyar su fadakar da mambobinsu kan kaurace wa amfani da sabis na kamfanonin sadarwa a lokutan da aka kayyade.
Kungiyar ta jaddada cewa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kare hakkokin ‘yan Najeriya kan karin farashin da ta ce bai dace ba.
I like what you guys are up also. Such clever work and reporting! Keep up the excellent works guys I have incorporated you guys to my blogroll. I think it’ll improve the value of my site 🙂