January 15, 2025

NITDA ta fara tura saƙon imel ga waɗanda suka nemi shiga shirinta na 3MTTT

0
IMG-20231107-WA0023.jpg

Daga Usama Taheer Maheer

Ga duk wanda NITDA ta tura wa saƙon imel ya san cewa fa dole sai ya nutsu ya karanta duk bayanai da ke cikin saƙon, shi ne zai sa ya san me zai yi gaba.

Da farko dai a duk imel ɗin da suke turawa akwai wani link a jiki wanda zai kai ka website ɗinsu kai-tsaye.

Daga nan sai ka sa imel ɗinka wanda ka yi amfani da shi wajen cike furogiram ɗin (ku lura sosai harafin farko dole ya kasance da ƙaramin baƙi ne—idan ka sa babban baƙi ba zai yi ba.

Misali “Usamahmaheer91@gmail.com” ba zai yi ba sai dai “usamahmaheer91@gmail.com shi ne daidai.”

Bayan ka sa imel ɗinka za su ba ka zaɓi a kan kai “Fellow” ne ko “Training Provider” (TP). Fellow shi ne ɗalibi TP kuma shine malami. Idan kai ɗalibi ne sai ka zaɓi Fellow.

Daga nan za su tura ma OTP ta imel ɗinka, wanda za ka je ka ɗebo lambobin sai ka saka a gurin.

Kai-tsaye za ka gan ka a cikin account ɗinka na website ɗin. Sai ka yi scrolling zuwa ƙasa za ka ga inda za ka ɗauki kwas ɗin da kake so ka yi. Idan wanda ka zaɓa da, bai makaba sai ka canza.

A ƙasa kuma akwai wasu tambayoyi da za ka shiga ka cike. Kamar na jarabawa ne, guda 13, amma a minti goma ake so ka gama amsawa. Kada ka tada hankalin a kan sai ka amsa daidai. Kawai ka yi iya iyawarka. Waɗannan tambayoyin su ne za su ba su damar sanin kaifin ƙwaƙwalwarka sai su saka ka inda ya dace da kai.

Daga nan za su sanar da kai cewa zuwa 15 ga watan Nuwamba za su fara turawa waɗanda suka yi nasarar shiga sahun farko saƙo.

Amma da kaso 1 kawai za su fara, wanda ya kama mutum dubu talatin ke nan. Kada ka karaya idan ba ka ga sunanka a karon farko ba. Ka yi haƙuri saboda mutane miliyan 3 ake sa ran banwa horon.

Daga ƙarshe akwai wani link da suka saka wanda zai kai ka ga wani kwas wanda yake da muhimmanci sosai mai taken Introduction to AI.

Idan ka kammala kwas ɗin za a ba ka satifiket.

Allah ya bada sa’a.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *