Nijar: Sojoji Za Su Gudanar da Taro Kan Dawo da Mulkin Dimokraɗiyya

Hukumomin mulkin sojin Nijar sun shirya babban taro kan shirin mayar da mulkin dimokraɗiyya, kusan shekara biyu bayan kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum.
Za a gudanar da taron na kwanaki huɗu a cikin watan Fabrairu, inda ake sa ran za a miƙa shawarwari ga shugaban mulkin sojin ƙasar, Janar Abdourahamane Tiani, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito.
Hukumar da ke da alhakin shiryawa za ta tattara rahoto tare da gabatar da shi a watan Maris.
Nijar na cikin ƙasashen yankin Sahel da sojoji suka karɓi mulki, kuma tare da Mali da Burkina Faso, sun yanke hulɗa da Faransa da ECOWAS.