Netanyahu ya sha alwashin ci gaba da kisar gilla a Gaza
Daga Sabiu Abdullahi
Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya bayyana cewa yakin da kasarsa ke yi a Gaza, wanda ya kai shekara guda, zai ci gaba da gudana muddin kasarsa tana fuskantar barazana.
Ya bayyana cewa ba zai yiwu a dakatar da hare-haren da Isra’ila ke kaiwa Gaza, Lebanon, da wasu yankunan Gabas ta Tsakiya ba, domin suna fafatawa da abokan gaba.
“Wannan nauyi ne da ya rataya a wuyanmu, ba za mu dakata ba sai mun kammala aikin da ya wajaba a kanmu,” in ji Netanyahu yayin jawabin da ya gabatar ga ‘yan kasar bayan zagayowar ranar 7 ga Oktoba, lokacin da Hamas ta kai harin ramuwa kan Isra’ila.
A lokaci guda, Isra’ila ta ci gaba da kai hare-hare a birnin Beirut na Lebanon, yayin da kungiyar Hezbollah ta harba rokoki sama da 100 zuwa Isra’ila a jiya, Litinin.
Instagram takipçi SEO optimizasyonu sayesinde daha fazla müşteri web sitemizi buluyor. https://royalelektrik.com//beylikduzu-elektrikci/