June 14, 2025

NDLEA ta kama wata mata da ta ɓoye ƙwayoyi a cikin al’aurarta

FB_IMG_1746976174806

Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) ta kama wata mata mai suna Ihensekhien Miracle Obehi, wadda ta yi yunkurin fitar da miyagun ƙwayoyi zuwa ƙasar Iran ta hanyar boye su a jikinta da kuma cikin jakarta.

An kama Obehi ne a filin jirgin sama na Port Harcourt da ke Jihar Rivers a ranar Lahadi, 3 ga Mayu, 2025, yayin da take shirin hawa jirgin Qatar Airline zuwa Iran ta hanyar Doha.

Obehi ta rufe kanta da hijabi domin kauce wa tsauraran binciken tsaro, amma jami’an hukumar sun cafke ta bayan samun bayanan sirri.

Binciken da aka gudanar ya gano cewa ta boye ƙwayoyi guda uku a cikin al’aurarta, sannan ta ɗora wasu kunsoshin ƙwayoyi biyu a cikin jakarta.

Baya ga haka, ta hadiye ƙwayoyi 67 na hodar iblis, waɗanda su ne kwayoyi masu hatsarin gaske na Class A.

An sanya ta a karkashin kulawa ta musamman, inda daga bisani ta fitar da dukkanin kunsoshin ƙwayoyin da ta hadiye.

Ta bayyana cewa an umurce ta da ta hadiye ƙwayoyi 70, amma bayan ta ci 67 ba ta iya ci gaba ba, lamarin da ya sa ta saka sauran guda uku a cikin al’aurarta. Jimillar nauyin ƙwayoyin da aka samo daga jikinta ya kai kilo 2.523.

NDLEA ta ce za a gurfanar da wadda ake zargin a gaban kotu da zarar an kammala bincike.