January 13, 2025

NDLEA ta kama hodar ibilis da aka ɓoye a cikin takalmi

120
image_editor_output_image-163628296-1720962525272.jpg

Daga Sabiu Abdullahi

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) ta gano wasu tarin hodar ibilis da aka boye a cikin tafin takalmin da aka nufi Turai da shi.

A wani bincike na daban, an gano kwayoyin tramadol a boye a cikin kwantena.

Daraktan yada labarai da bayar da shawarwari na hukumar, Femi Babafemi, ya saka bidiyon haramtattun kwayoyin da aka kama a kan shafin X com ranar Lahadi.

Hukumar ta gargadi matafiya da su yi taka-tsan-tsan wajen karbar jakunkuna ko kayayyaki daga hannun wasu domin ba su san abin da ke ciki ba.

Da yake ɗaura faifan bidiyon, ya rubuta, “Bidiyon farko ya nuna lokacin da jami’an #ndlea_nigeria suka gano buhunan hodar ibilis a tafin takalmi zuwa Turai yayin da na biyun ya nuna yadda aka gano kwayoyin tiramadol da aka boye a cikin kwantena.

“Wannan dalili ne da ya sa dole ne ku yi taka tsantsan da duk wata jaka da aka ba ku don tafiya da ita.”

120 thoughts on “NDLEA ta kama hodar ibilis da aka ɓoye a cikin takalmi

  1. купить диплом о высшем образовании в санкт петербурге [url=https://landik-diploms.ru/]купить диплом о высшем образовании в санкт петербурге[/url] .

  2. <a href=http://szotar.sztaki.hu/en/node/add/forum?gids=270123/>Легальная покупка диплома о среднем образовании в Москве и регионах

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *