NDLEA ta cafke wani manomin ganyen wiwi a Sokoto
Daga Sabiu Abdullahi
Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa reshen jihar Sokoto, a ranar Juma’a, ta kama wani Anas Sani mai shekaru 32, wanda aka gano yana noma ganyen wiwi a jihar.
A nasa jawabin kwamandan hukumar na jihar, Iro Adamu, ya ce an gano lamarin ne a daren Juma’ar da ta wuce a unguwar Sanyinna da ke karamar hukumar Tambuwal a jihar, bayan samun rahoton sirri.
“An dasa ta ne a gonar masara ta yadda masananta ne kawai su iya fahimtar mece ce.
“Irin wiwin na kasashen waje wanda ke da matukar tasiri da tsada,” in ji shi
Adamu ya kara da cewa, wannan shi ne karon farko da aka gano irin wannan gona a jihar, wanda a cewarsa, ya yi kira da a gudanar da gangami da kuma sintiri don hana jama’ar yankin shiga haramtacciyar sana’ar.
Wanda ake zargin yana ‘ya’ya biyu, kuma yayin da yake zantawa da manema labarai, ya ce ya koyi sana’ar ne a lokacin da yake da kantin sayar da kayayyaki a jihar Legas.
“Ni farkon fara kasuwancin nan ke nan. Na koye shi ne lokacin da nake zaune a Legas kuma na yanke shawarar gwada shi a garinmu na Sanyinna,” in ji Anas.




