NCDC Ta Gargaɗi ‘Yan Nijeriya Kan Tafiya Uganda Saboda Bullar Cutar Ebola

Hukumar Yaƙi da Cututtuka Masu Yaɗuwa ta Nijeriya (NCDC) ta shawarci ‘yan ƙasa da su guji tafiye-tafiye zuwa Uganda, sakamakon bullar cutar Ebola da aka tabbatar a ƙasar.
Wannan gargaɗi na NCDC ya biyo bayan sanarwar da Ma’aikatar Lafiya ta Uganda ta fitar a ranar 30 ga Janairu, 2025, inda ta bayyana cewa an samu barkewar nau’in cutar Ebola mai suna Sudan a gundumomin Wakiso, Mukono, da Mbale.
Duk da cewa NCDC ta tabbatar da cewa ba a samu rahoton bullar cutar a Nijeriya ba, a baya Ma’aikatar Lafiya ta Uganda ta bayyana cewa cutar ta hallaka mutum guda, yayin da ake binciken wasu mutane 44 da ake zargin sun yi mu’amala da shi.
Wannan ne karo na tara tun daga shekarar 2000 da aka samu bullar cutar Ebola a Uganda, ƙasar da ke yankin Gabashin Afirka.
Sanarwar NCDC ta bayyana cewa hukumar na ci gaba da sa ido a wuraren shige da fice na Nijeriya, tare da sabunta matakan bayar da agajin gaggawa da hanyoyin bincike don gano cutar a manyan ɗakunan gwaje-gwaje da ke manyan biranen da ke da filayen jiragen sama na ƙasa da ƙasa.
Kolay bahis siteleri 🚀 Şansını Çevir, Kazançlar Seni Bekliyor! https://kusadasi-winsome.tumblr.com/