December 7, 2025

NCC ta ce 14 ga watan Satumba ne wa’adin ƙarshe na haɗa layukan waya da NIN

images (10) (13)

Daga Sabiu Abdullahi

Hukumar sadarwa a Najeriya (NCC) ta fitar da sanarwar ba da wa’adin ƙarshe na hada layukan waya da NIN.

Wata sanarwa da hukumar ta fitar a yau Laraba ta ce ta ba wa kamfanonin sadarwar umarnin kammala haɗa layukan da NIN ɗin zuwa ranar 14 ga watan Satumban 2024.

Idan ba a manta ba, a shekarar 2020 ne hukumar ta fito da tsarin haɗa lambar ta ɗan ƙasa da layukan waya tana mai cewa zai taimaka wajen daƙile aikata laifuka.

Tun daga lokacin ne kuma ta dinga saka lokacin rufewa tana ɗagawa har zuwa yanzu.

Sai dai hukumar ta ce wannan ne karo na ƙarshe da za ta ɗaga wa’adin.