May 17, 2025

NBS: Hauhawar Farashi Ta Kai Kashi 24.48 a Janairu Bisa Sabon Tsarin Ƙididdiga

images-2025-02-18T140319.518.jpeg

Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS) a Najeriya ta bayyana cewa hauhawar farashi ya tsaya kan kashi 24.48 cikin 100 a watan Janairu da ya gabata.

Wannan ne karon farko da NBS ke fitar da rahoton bisa sabon tsarin tattara alƙaluma da ta fara amfani da shi. Saboda haka, da wuya a tantance haƙiƙanin raguwar ko ƙarin hauhawar farashi a yanzu.

Rahoton ya nuna cewa hauhawar farashin kayan abinci ya kai kashi 26.08 cikin 100 idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata.

A cewar shugaban hukumar, Prince Adeyemi Adeniran, wanda ya yi bayani a ranar Talata, sun sauya tsarin ne domin daidaita shi da matakan ƙasashen duniya.

Ya bayyana cewa karo na ƙarshe da Najeriya ta canza tsarin ƙididdigar farashin kaya shi ne a shekarar 2009, inda ake amfani da bayanan kayayyakin da aka fi saye a lokacin.

Sabon tsarin zai maye gurbin tsohon tsarin, inda a yanzu za a dinga lissafa hauhawar farashi bisa bayanan da aka tattara daga shekarar 2024, maimakon 2009 da aka riƙa amfani da shi a baya.