Najeriyar ta yi asarar sama da tiriliyan 4 saboda satar ɗanyen mai
Daga Sabiu Abdullahi
Gwamnatin Tarayya, a ranar Litinin, ta bayyana cewa an sace ɗanyen mai na sama da Naira tiriliyan 4.3t a cikin wasu bututun mai guda 7,143 a cikin shekaru biyar.
Ta bayyana hakan ne a taron fasahar bututun mai na kasa da kasa da aka yi a Abuja, mai taken ‘Boolstering Regulations, Technology and Security for Growth.’
Kungiyar ƙwararru a kan bututun mai ta Najeriya ce ta shirya taron.
A jawabin da kungiyar ‘Nigerian Extractive Industries Transparency Initiative’, wata hukumar gwamnatin tarayya ta gabatar a wurin taron, kungiyar ta bayyana cewa satar man fetur da asarar da ake yi a Najeriya ya zama wani lamari da ke buƙatar ɗauki na gaggawa.
Sakataren zartarwa na NEITI, Ogbonnaya Orji, ya ce satar mai wani lamari ne na babba wanda ke haifar da babbar barazana ga haƙo man fetur tare da babban illa ga ci gaban tattalin arziki, kasuwanci da ribar da kamfanonin mai ke samu.
Da yake bayar da bayanai daga rahotannin hukumar da ke tabbatar da ikirarin nasa, ya ce: “NEITI ya bayyana cewa a cikin shekaru biyar da suka gabata, 2017 zuwa 2021, Najeriya ta samu rahoton fasa bututun mai guda 7,143 da kuma ɓarna da gangan wanda ya yi sanadin satar danyen mai da asarar kayayyaki na ganga miliyan 208.639 da aka kiyasta darajarsu a kan kuɗi $12.74m ko N4.325tn.
“Rahotanni na NEITI sun kuma bayyana cewa a cikin wannan lokaci Najeriya ta kashe N471.493bn wajen gyara ko kula da bututun mai.”
Orji ya yi nuni da cewa, daga rahoton masana’antun mai da iskar gas na NEITI na shekarar 2021 da aka fitar a watan Satumba, fannin ya kai kashi 72.26 na adadin kuɗin da Najeriya ke fitarwa da kuma kuɗaɗen da gwamnati ke samu, kashi 40.55 na kudaden shiga na gwamnati, sannan ya samar da ayyuka ga mutane 19,171.