February 10, 2025

Najeriya Ta Karɓo Dala Miliyan 53 Na Dukiyar Da Aka Zargi Diezani Ta Ɗiba

1
images-2025-01-10T130457.695.jpeg

Daga Sabiu Abdullahi

Gwamnatin Najeriya ta karɓo dukiya ta dala miliyan 52.88 da aka danganta da tsohuwar Ministan Albarkatun Man Fetur, Diezani Alison-Madueke.

Amurka ce ta dawo da dukiyar da aka fi sani da “Galactica assets.”

A cewar Ministan Shari’a kuma Babban Lauyan Tarayya, Lateef Fagbemi, za a yi amfani da kuɗaɗen wajen ayyukan raya ƙasa.

An tsara cewa dala miliyan 50 za a yi amfani da su wajen ayyukan samar da wutar lantarki a karkara ta hannun Bankin Duniya, yayin da sauran dala miliyan 2.88 za a bai wa Cibiyar Kasa da Kasa ta Shari’a domin ƙarfafa tsarin shari’a da yaƙi da cin hanci da rashawa.

Fagbemi ya bayyana cewa dawo da wannan dukiya wani babban ci gaba ne a haɗin gwiwar da ke tsakanin Najeriya da Amurka wajen yaƙi da cin hanci da tabbatar da bin doka.

Ya kuma ce hakan yana nuna ƙudurorin Shugaba Bola Tinubu na magance matsalar rashawa a ƙasar.

1 thought on “Najeriya Ta Karɓo Dala Miliyan 53 Na Dukiyar Da Aka Zargi Diezani Ta Ɗiba

  1. I like what you guys are up too. Such intelligent work and reporting! Carry on the excellent works guys I have incorporated you guys to my blogroll. I think it will improve the value of my website :).

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *