Najeriya ta fara harƙallar tatacce da ɗanyen mai da naira
Daga Sabiu Abdullahi
Gwamnatin Najeriya ta sanar da fara sayar da ɗanyen mai da tataccen mai cikin gida ta amfani da kuɗin ƙasar, naira.
Wale Edun, Ministan kuɗi da tattalin arziki, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da Ma’aikatar Kuɗi ta wallafa a shafinta na X ranar Asabar.
Sanarwar ta ce sayar da ɗanyen mai da kuɗin naira ya fara ne tun daga ranar 1 ga watan Oktoba.
Ministan ya ce wannan mataki na cikin manufofin gwamnatin Bola Tinubu da ake sa ran zai inganta tattalin arzikin ƙasa, samar da zaman lafiya, da kuma ƙaruwar dogaro da kai.
Edun ya kara da cewa Najeriya za ta ci gaba da bin matakan da suka dace wajen lura da yanayin kasuwannin ɗanyen mai a duniya don inganta ci gaban ƙasar.
Wannan mataki ya biyo bayan amincewar majalisar zartarwa mako tara da suka gabata ga ƙudurin Shugaba Tinubu na umartar Kamfanin NNPCL da ya sayar wa matatar mai ta Dangote da sauran matatun cikin gida ɗanyen mai cikin kuɗin naira.
Masu sharhi sun bayyana cewa sayar da mai da naira zai rage farashin dala, wanda hakan zai taimaka wajen sauƙaƙa tsadar rayuwa a ƙasar.