Najeriya ta dawo amfani da tsohon takenta
Daga Sodiqat Aisha Umar
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya amince da dokar dawo da amfani da tsohon taken Nahiyar mai suna “Nigeria: We Hail Thee”.
Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio ne ya bayyana hakan yayin zaman majalisar a jiya laraba, wanda tuni aka yi amfani da shi lokacin da Tinubu ya yi wa taron majalisar na haɗin gwiwa jawabi a jiya Laraba.
Shi ne karon farko da majalisar ta rera taken tun bayan daina amfani da shi shekara 46 da suka wuce.
Shugaba Tinubu ya ce taken na nuna bambancin al’adu, da kuma wakiltar kowane ɓangare tare da zimmar taka rawa wajen ƙulla ‘yan’uwantaka.
Yayin bikin cikarsa shekara ɗaya a kan mulki da kuma murnar cika shekara 25 da komawa mulkin dimokuraɗiyya, shugaban ya taya ‘yan ƙasa murna kuma ya nemi ‘yan majalisa “su ci gaba da aiki tare don gina ƙasar da na gaba za su yi alfahari da ita”
Dokar Taken Ƙasa ta 2024, wadda za ta bai wa ƴan Najeriya damar komawa amfani da tsohon taken ƙasar.
A lokacin zaman da majalisar ta gudanar, wanda shugaban na Najeriya ya halarta, ƴan majalisar sun rera taken.
Dokar ta tanadi cewa ma’aikatar yaɗa labaru ta Najeriya za ta “tsara yadda za a riƙa rera taken na Najeriya, kuma za su naɗi sabon taken wanda za a riƙa kunnawa.
Za a wallafa sabon taken Najeriyar da aka naɗa a shafukan intanet na gwamnati kuma zai kasance cikin abubuwan da za a rika koyar da ɗalibai a makarantu.
A shekarar 1960 ne Najeriya ta amince da fara amfani da tsaken Najeriya lokacin da ta samu ƴancin kai, sai dai daga baya a n daina amfani da shi a shekarar 1978, lokacin mulkin shugaban mulkin soji Olusegun Obasanjo