April 19, 2025

Najeriya ce ta 102 a jerin ƙasashe masu farin ciki a duniya

images-259.jpeg

Daga Sabiu Abdullahi

Wani sabon rahoton ya sanya Najeriya a matsayin kasa ta 102 da ta fi farin ciki a cikin kasashe 143.

Rahoton, wanda TheCableIndex ya tattara, ya bayyana matsayin da aka samu a kan abubuwa daban-daban da ke ba da gudummawa ga jin daɗin jama’a da gamsuwa a rayuwa.

Kasashen da ke kan gaba su ne kasashen Nordic, inda Finland ke kan gaba, sai Denmark da Iceland.

Jerin ya haɗa da ƙasashe kamar Sweden, Norway, da Netherlands, waɗanda aka sani da ingancin rayuwa da tsarin jin daɗin jama’a.

Isra’ila kuwa, wacce aka santa da al’adunta da ci gaban fasaha, ta shiga matsayi na 5, wanda ke nuna cuɗanya na zamani da dabi’un gargajiya.

A halin yanzu, ƙasashe kamar Switzerland, Ostiraliya, da New Zealand su ma sun yi fice a cikin manyan matsayi.

Sanya Najeriya a matsayi na 102 kuwa ya haifar da tambayoyi game da abubuwan da ke tasiri a rayuwar ‘yan kasarta.

Yayin da ƙasar ke da ɗimbin al’adu daban-daban da albarkatu masu yawa, ƙalubale kamar tabarbarewar tattalin arziƙi, matsalolin tsaro, da rashin daidaiton zamantakewa na iya taimakawa wajen rage darajarta.

Sauran kasashen Afirka ma sun fito a cikin rahoton, inda Kenya ta zo ta 114, Benin a matsayi na 116, Ghana a matsayi na 120, sai Togo a matsayi na 124.