February 10, 2025

NAFDAC Ta Rufe Kanti A Abuja Saboda Rashin Bin Ka’ida

1
images-95.jpeg

Daga Sabiu Abdullahi

Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Nijeriya (NAFDAC) ta rufe wani babban kanti mallakar ‘yan China a ranar Litinin, bisa zargin sayar da kayayyakin da ke ɗauke da tambarin rubutun Sinanci ba tare da sahalewar hukumar ba.

Rahoton Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya bayyana cewa wannan kanti na cikin unguwar Wuse 2, Abuja, babban birnin ƙasar.

Daraktan da ke kula da bincike a NAFDAC, Shaba Mohammed, ya shaida wa manema labarai cewa galibin kayayyakin da ake sayarwa a kantin suna ɗauke da tambarin rubutun Sinanci, wanda ya saɓa wa dokokin hukumar.

Har ila yau, Shaba Mohammed ya bayyana cewa wasu daga cikin kayayyakin da ake sayarwa a kantin sun ƙare wa’adi, amma har yanzu ana ci gaba da sayar da su ga jama’a.

1 thought on “NAFDAC Ta Rufe Kanti A Abuja Saboda Rashin Bin Ka’ida

  1. I’m impressed, I have to say. Actually not often do I encounter a weblog that’s each educative and entertaining, and let me let you know, you may have hit the nail on the head. Your concept is outstanding; the problem is something that not enough persons are talking intelligently about. I am very completely happy that I stumbled across this in my search for something relating to this.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *