NAFDAC ta garƙame shaguna 100 a Enugu kan zargin sayar da gurɓatattun kayan barasa
Daga Abdullahi I. Adam
Hukumar kula da abinci da magunguna ta ƙasa, NAFDAC ta garƙame shaguna kusan 100 a shahararriyar kasuwar Ogbete da ke jihar Enugu a kudancin Najeriya bisa zargin cewa masu shagunan na sayar da gurɓatattun kayan barasa.
Banda wannan, hukumar ta sami nasaran damƙe wasu ‘yan kasuwa su 4 gami da kame wata mota da ke cike maƙil da lalatattun kayan masarufi.
A zantawarsa da manema labaru a jiya Litini bayan kai samamen, babban daraftan hukumar a yankin kudu maso-gabas, Martins Iluyomade ya ce tuni suna tsare da waɗanda ake zargin kuma za’a garzaya da su kotu da zarar an kammala bincike kan lamarin.
Iluyomaden ya ce irin wannan samame a kan gudanar da shi ne don ƙarfafa ayyukan hukumar na tabbatar da lafiyar al’umma tare da tsaftace yankin daga lalatattun kayayyaki da kuma jabun ababen masarufi.
“Mun dira a shahararriyar kasuwar Ogbete da ke Enugu ne tun ranar Juma’a, kuma mun sami nasaran garƙame shaguna 100 da ke sayar da gurɓatattun kayan barasa.
“Mun rigaya mun cafke waɗanda ake zargi, kuma tuni bincike ya yi nisa.”
Irin waɗannan gurɓatattun kayan barasa da ake sayar ma al’umma bai dace ba, kuma mun himmatu wajen tsaftace kasuwar daga irin waɗannan miyagun kaya.” inji shi.
Daraftan na NAFDAC ya ce samamen da su ke yi na haɗin-gwiwa ne wanda ‘yansanda, sojoji da kuma sauran jami’an tsaro ke ba goyon baya.