Mutumin Bauchi ya samar da injin shuka
![IMG-20240523-WA0008.jpg](https://tcrhausa.com/wp-content/uploads/2024/05/IMG-20240523-WA0008.jpg)
Daga Abdullahi I. Adam
Wani bawan Allah mazaunin Bauchi ya yi hikimar samar da injin zamani wanda zai sawwaƙa ma manoma wajen shukan masara da shinkafa.
Mutumin mai suna Ukasha Safwan ya bayyana, a shafin Facebook, cewa wannan inji da ya ƙirƙira mai sauƙin sarrafawa ne, kuma zai iya shuka kuyyoyi biyar na masara a tafiya ɗaya.
Injin zai iya shuke eka biyu a wuni guda, kamar yadda wanda ya samar da shi ya bayyana.
![](https://tcrhausa.com/wp-content/uploads/2024/05/fb_img_17164450604152327106985925628753-225x300.jpg)