January 15, 2025

Mutum miliyan 1.6 sun nemi bashin CREDICORP, inji Nwagba

0
IMG-20240515-WA0006.jpg


Daga Abdullahi I. Adam

Babban Manaja kuma Babban Jami’in Zartarwa na Hukumar Kula da Kare Kayayyakin Kasuwa wato CREDICORP, Uzoma Nwagba, ya bayyana cewa a yanzu haka mutum miliyan 1.6 ne suka nemi bashin CREDICORP wanda gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta ƙaddamar a watan Afrilu da ya gabata.

An ƙaddamar da kashi na farko na bashin na Consumer Credit Scheme ne a ranar 21 ga Aprilu inda Shugaba Tinubu ya bayyana cewa shirin zai bai wa ‘yan ƙasa masu aiki damar samun lamuni don sayayyar kayayyakin da suke buƙata don rayuwar yau-da-kullum.

Nwagba ya ce “ba mu zaci yawan masu rubuta takardun buƙata da kuma bayyana sha’awar hakan zai kai haka lokacin da muka fitar da EoI kamar mako guda bayan an naɗa ni ba,” kamar yadda ya bayyana a wata hira da gidan talabijin na Channels Television a shirinsu  mai suna Politics Today.

Shugaban Tinubu ya naɗa Nwagba ne a matsayin shugaban CREDICORP a ranar 5 ga Aprilu, kuma aikin hukumarsa samar da hanyoyin bada lamuni ga ma’aikata don sauƙaƙa da faɗaɗa samun bashi kamar yadda ake sa ran hukumar ta soma aiwatarwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *