Mutum 45,689 Ne Ke Neman Samun Aiki Da NNPCL
Daga Sabiu Abdullahi
Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPCL) ya fara gudanar da gwajin kwarewa ta kwamfuta ga mutum 45,689 da ke neman guraben aiki daban-daban a kamfanin.
An shirya gwajin ne a cibiyoyi daban-daban a fadin Najeriya, wanda ke zama mataki na biyu a tsarin daukar ma’aikatan.
A cikin wata sanarwa da NNPCL ta wallafa a shafinta na Facebook, kamfanin ya sake jaddada kudirinsa na yin tsarin daukar ma’aikata cikin gaskiya da adalci.
Sanarwar ta ce: “Yayin da ake fara gwajin ƙwarewa ta kwamfuta na ɗaukar ma’aikata a NNPC Ltd. yau a cibiyoyi daban-daban a fadin kasar, mutum 45,689 suna fafutukar samun guraben aiki a tsarin da ke cike da gaskiya da adalci.”
Shugaban Rukunin NNPCL, Mele Kyari, wanda ya ziyarci daya daga cikin cibiyoyin gwajin, ya tabbatar wa masu neman aikin cewa tsarin zai kasance mai sauki, gaskiya, adalci, da inganci.
Ya kuma bayyana cewa an tanadi kayayyaki na musamman don tabbatar da cewa masu naƙasa za su iya gudanar da gwajin ba tare da wata matsala ba.




