Mutanen Nijeriya kimanin miliyan 32 za su fuskanci matsananciyar yunwa
Daga Sodiqat Aisha Umar
Akwai yiyuwar akalla ‘yan Najeriya miliyan 32 za su fuskanci wani yanayi mai kama da matsananciyar yunwa a tsakanin watanin Yuni da Agustan bana matuƙar ba a ɗauki matakan gaggawa ba.
A cewar rahoton Kwamitin Kai Ɗauki na Ƙasa da Ƙasa IRC, adadin mutanen da za su fuskanci matsalar ƙarancin abinci a yankunan yammaci da tsakiyar nahiyar Afirka a wannan dan tsakani zai kai kimanin mutane miliyan 52 kwatankwacin kaso 12 cikin 100 na mutanen da aka tantance.
Kasashen da al’amarin zai shafa sun hadar da Mauritaniya (inda zai shafi mutane 656, 652, kwatankwacin kaso 14 cikin 100) da Burkina Faso (inda zai shafi mutane 2, 734, 196, kwatankwacin kaso 12 cikin 100) da Nijar (inda zai shafi mutane 3, 436, 892, kwatankwacin kaso 13 cikin 100) da Chadi (inda zai shafi mutane 3, 364, 453, kwatankwacin kaso 20 cikin 100) da Saliyo (inda zai shafi mutane 1, 569, 895, kwatankwacin kaso 20 cikin 100) da kuma Najeriya (inda zai shafi mutane 31, 758, 164, kwatankwacin kaso 16 cikin 100).
Har ila yau, rahoton ya kara da cewar matsalar karancin cimakar za ta fi kamari a jihohin Arewacin Najeriya irinsu Sakkwato da Zamfara inda fashin bakin da aka yi ya bayyana yanayin da mai matukar tsanani, har ma fiye da kaso 15 cikin 100 na kananan yara za su yi fama da cutar tamowa da karancin abinci ke haddasawa.
Rahoton na IRC ya alakanta dalilan tsanantar matsalar karancin cimakar a yankin sahel ga matsalolin rashin tsaro da sauyin yanayi da kuma tabarbarewar tattalin arzikin kasashe, musamma ma matsalar hauhawar farashin kayan masarufi.