March 28, 2025

Mutanen gari sun ƙona gida da motar mutumin da ya yi ɓatanci ga Fiyayyen Halitta

images-102.jpeg

Ana zaman dar-dar a jihar Katsina sakamakon hatsaniya da ta tashi a shafukan sada zumunta inda ake zargin wani Kirista mai suna Mani Abubakar ya yi batanci ga addini.

Rubutu ne dai da aka wallafa a Facebook, wanda ake kallonsa a matsayin cin zarafi ga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama, ya tayar da hankali.

Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya ta’azzara ne lokacin da wasu mutane suka banka wa gidan Abubakar wuta da kuma motarsa.

Daga nan sai Abubakar ya yi nasarar tserewa daga gidansa da ke Babaruga.

A cewar mataimakin shugaban Ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya a Katsina, Muyiwa Segun, an shawo kan lamarin sakamakon daukar matakan gaggawa da kwamishinan ‘yan sandan jihar, Aliyu Musa ya dauka.

Wannan dai ba shi ne karo na farko da ake zargin batanci a yankin na Arewa maso Yammacin Najeriya ba.

Ko a shekarar da ta gabata ma sai d aka yi wa wata mai Suna Deborah kisar taron dangi saboda wasu munanan kalamai a kan Fiyayyen Halitta.